Yadda dan majalisar tarayya yasha da kyar a Zariya

0
256

Wani Dan Majalisar Dattawa Ya Sha Da Kyar A Anguwar Jushin dake karamar hukumar Zaria ta jihar Kaduna.

Hon. Dakta Abbas Tajuddeen (Iyan Zazzau) Dan majalisa ne mai Wakiltar Mazabar Karamar Hukumar Zaria.

Dan majalissar Wakilan ya sha da kyar ne a ranar lahadin da ta gabata a Anguwar (Jushin Ciki) in da daruruwar matasan Anguwar suka rakashi da cewa “ba ma so, ba ma yi” a wani faifan bidiyo da wakilinmu ya samu.

Dakta Abbas Tajuddeen wanda ake kira ‘Teejay’ ya shiga Anguwar (Jushin Ciki) ne domin duba wani fili da mutanen Anguwar su ka siya don gina Asibiti.

A cewar matasan, sunyi hakane sabida halin ko in kula da dan majalisar ya nuna musu,  “tunda ya tafi Abuja ya manta da su sai yanzun da zabe ya sake karatowa”,
Wasu jaruman matasa ne suka kare dan majalisa Abbas ya tsira da rayuwarsa.

Hakan yasa wakilinmu ya nemi jin ta bakin Dan majalisar ta wayarsa amma lamarin ya cutura.

Haka zalika wakilinmu ya tura sako tawaya ga mai taimakamashi na musamman, malam Iliyasu Balarabe shima lamarin ya cutura.

Yanzu haka jama’ar anguwar jushi sun sha damarar kada Dan majalisar a kujerarsa da yake neman komawa a wannan zabe mai zuwa.

Leadership Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here