JAMB ta tsawaita lokacin rajistar jarrabawar 2023 da mako guda

0
109

Hukumar shirya jarabawar shiga jami’a ta tsawaita rijistar jarrabawar shekarar 2023 da mako guda.

An fara tsawaita wa’adin ne daga ranar Laraba, 15 ga Fabrairu, 2023. Koyaya, siyar da ePINs zai ƙare a ranar 20 ga Fabrairu, 2023, yayin da rajistar UTME zai ƙare ranar Laraba, 22 ga Fabrairu, 2023.

Shugaban sashen hulda da jama’a na hukumar JAMB, Dr Fabian Benjamin ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Abuja. Sanarwar ta kara da cewa, “A karshen sayar da e-PINs a ranar Talata, 14 ga Fabrairu, 2023, dalibai 1,527,068 sun yi nasarar yin rajistar jarrabawar ta shekarar 2023 da suka hada da 168,748, wadanda suka nuna sha’awarsu ta daukar jarrabawar Mock Kimanin dalibai1,527,068 ne suka yi nasarar yin rijistar jarabawar UTME ta shekarar 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here