Kotu ce za ta raba ni da INEC – Obi

0
59

Dan takarar shugaban kasa na Najeriya a ɗaya daga cikin manyan jam’iyyun hamayya, Labour Party, Peter Obi ya ce shi ne ya ci zaɓen da aka yi ranar 25 ga watan Fabarairu 2023.

A cewarsa zai bi duk wani matakin shari’a domin ya ƙwato nasararsa.

Mista Obi ya ce wannan ne karon farko da ya fito duniya yake magana tun bayan kada kuri’ar da ya yi a zaɓen, saboda haka ya ce duk wani sako ko magana da aka danganta da shi a baya ba shi ya fada ba.

“Mun ci zaɓen kuma za mu tabbatar wa da ‘yan Najeriya hakan,” in ji Obi.

Ɗan takarar na jam’iyyar Labour ya ce har yanzu yana nan a kan bakansa na burin samar da sabuwar Najeriya.

Sannan ya yi kira ga dukkanin ‘yan ƙasar da kada su gajiya kuma kada su karaya, su tabbatar sun je sun shiga an dama da su a zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisar dokokin jihohi da za a yi ranar 11 ga watan Maris.

Mista Obi ya ce ba wata haɗaka da yake yi da wata jam’iyya a yanzu amma yana tare da dukkanin ‘yan Najeriya da ransu ya ɓaci kuma suka damu kan yadda sakamakon zaɓen ya kasance.

Ɗan takarar jam’iyya mai mulki, APC, wato Bola Ahmed Tinubu, shi ne ya yi nasara a zaɓen shugaban ƙasar inda ya samu ƙuri’a miliyan 8.79, wato kashi 37 cikin ɗari na ƙuri’un da aka kaɗa.

Sai Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP wanda ya zo na biyu, da ƙuri’a 6,984,520, wato kashi 29.07 cikin ɗari.

Yayin da Peter Obi ya zo na uku da ƙuri’a 6,101,533, wato kashi 25.4 cikin ɗari.

Ƙasar mafi ƙarfin tattalin arziƙi a Afirka, tana da al’ummar da ta zarta miliyan 200.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here