Dan Ronaldinho, Joao Mendes ya kulla yarjejeniya da Barcelona

0
54

Dan tsohon tsauraron Barcelona Ronaldinho wato Joao Mendes ya kulla kwantiragi da kwalejin horar da matasan ‘yan wasan Barcelona wanda zai bashi damar taka leda tare da ‘yan wasan kungiyar, tawayar ‘yan kasa da shekaru 19.

Mendes mai shekaru 18 ana ganin zai bi sahun mahaifinsa ne wanda ya shafe shekaru 5 yana taka leda da Barca.

Dan wasan wanda a baya ke taka leda da kungiyar kwallon kafa ta Cruzeiro wadda ke doka gasar Serie B ta bRazil ya kawo karshen kwantirtagin nasa ne bayan samun damar taka leda da kungiyar ta Barcelona don bin sahun mahaifinsa.

Rahotanni sun ce Mendes baiyi amfani da sunan mahaifinsa wajen samun kwantiragin da Barcelona ba, haka zalika ba da sunan mahaifinsa ya samu damar taka leda da Cruzeiro ba hasalima sai bayan tabbatuwar samun shiga kungiyar tukuna da dama suna san waye mahaifin shi.

Ronaldinho mai shekaru 42, tun bayan ritaya daga fagen tamaula, yanzu haka yana matsayin jakadan Barcelona ne.

Kwantiragin na Mendes nan una cewa matashin dan wasan zai samu horo a fitacciyar kwalejin La Masia wadda ta yaye ‘yan wasa irinsu Lionel Messi da Ferard Pique da kuma Xavi Henandes.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here