‘Yan bindiga sun sace matan sarki a jihar Taraba

0
53

Wasu masu satar mutane domin karɓar kuɗin fansa sun addabi al’ummar yankin Sarkin Kudu da ke ƙaramar hukumar Ibbi a Jihar Taraba, ta arewa maso gabashin Najeriya, inda a ranar Alhamis suka sace mutane ciki har da matan Sarkin biyu.

Bayanai sun nuna cewa al’ummomin yankin suna zaune cikin zullumi kan yadda a kwanakin nan ɓarayin mutanen suka addabe su.

Rahotanni sun ce a ranar Alhamis da daddare ne aka shiga garin aka sace matan Sarkin Kudu guda biyu kuma har yanzu babu labarinsu.

Mutanen yankin na Sarkin Kudu sun ce a yanzu ba sa samun yin barci cikin kwanciyar hankali saboda ƙaruwar ta’addancin masu garkuwa da mutanen.

Wani daga cikin makusantan sarkin garin ya yi wa BBC ƙarin bayani inda ya ce, a ranar Alhamis ɓarayin suka je gidan sarkin da nufin sace shi, amma ba su samu sa’a ba, sai suka yi gaba da matansa biyu.

Ya ƙara da cewa wannan matsala ta yi ƙamari shekara biyu da ta gabata a yankinnasu, amma sakamakon tsauraran matakai da gwamnatin jiha da ta ƙaramar hukuma da sauran jam’ian tsaro suka ɗauka sai ta lafa.

”Amma kuma yanzu abin ya sake dawowa inda a sati biyu ko uku da ya gabata an saci wani yaro, an dawo da shi aka kuma sake ɗaukar wani wanda ba a dawo da shi ba har yanzu.”

Ita ma wata mata da masu garkuwa da mutanen suka sace ‘ya’yanta biyu ta ce suna cikin wani hali na tashin hankali saboda ayyukan mutanen.

Ta gaya wa BBC cewa bayan da suka saci ɗanta ɗaya an biya kuɗin fansa sun sako shi sai kuma suka ƙara sace ɗaya, wanda har yanzu ba su sako shi ba, suna neman a ba su Naira miliyan 20 kafin su sako shi.

Bayanai sun ce ya zuwa yanzu jami’an tsaro da ‘yan sa-kai na cikin daji sun bi sawun mutanen a ƙoƙarin da suke yi na ganin sun kuɓuto da waɗanda aka yi garkuwa da su.

Sai dai BBC ta tuntuɓi mai magana da yawun ‘yan sandan jihar ta Taraba, SP Usman Abdullahi domin jin ƙarin bayan a kan lamarin, amma har zuwa lokacin rubuta wannan labari bai ɗauki kiran waya ba.

Jihar Taraba dai na cikin jihohi da ke fama da matsalar masu garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa musamman ma a yankin kudancin jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here