Wannan shafin zai rika kawo muku kammalallen sakamakon zaben gwamnoni da aka gudanar a jihohin Najeriya da Hukumar Zaben Kasar ta fitar da kanta.
Gwamna Mai Mala Buni na APC ya ci gaba da rike madafun iko bayan ya yi nasara a zaben gwamna na ranar Asabar da yawan kuri’u 317,113 , inda ya yi wa babban mai fafatawa da shi na jam’iyyar PDP, Alhaji Sharif Abdallah fintinkau wanda kuma ya samu jumullar kuri’u 104,259.
Jjihar Kwara
Sakamakon Hukumar INEC ya nuna cewa, gwamna mai ci na jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq na jam’iyyar APC, shi ne ya lashe zaben ranar Asabar da yawan kuri’u 273,424, inda ya doke babban abokin hamayyarsa na PDP, Alhaji Abdullahi Shu’aib Yaman wanda ya samu kuri’u 155,49490.
Jihar Gombe
Gwamna mai ci, Inuwa Yahya na jam’iyyar APC shi ne ya sake lashe zaben jihar Gombe daa yawan kuri’u 342, 821, inda Muhammad Baarde na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 233, 131.
Jihar Ogun
Hukumar zaben Najeriya ta ayyana Dapo Abiodun na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Ogun da yawan kuri’u 276,298, inda ya doke abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP, Ladi Adebutu wanda ya samu kuri’u 262,383.
Jihar Katsina
Hukumar zaben Najeriya INEC ta ayyana Dakta Dikko Umaru Radda na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaÉ“en gwamnan jihar Katsina.
Radda ya samu nasara ne da Æ™uri’u 859,892, yayin da mai biye masa Garba Yakubu Lado Danmarke na jam’iyyar PDP ya samu kuri’a 486,620.
Jami’in da ke tattara sakamakon zaÉ“en gwamnan a jihar ta Katsina, Farfesa Mu’azu Abubakar Gusau ne ya bayyana sakamakon a daren wannan Lahadi.
Jihar Jigawa
Mataimakin gwamnan jihar Jigawa kuma É—an takarar gwamnan a karkashin jam’iyyar APC mai mulki, Alhaji Umar Namadi ya lashe zaÉ“en gwamna da aka gudanar a ranar Asabar.
Namadi ya lashe zabe a ƙananan hukumomi 26 daga cikin 27 na jihar.
Ya samu nasarar ce da kuri’u 618,449 yayin da dan takarar jam’iyyar PDP, Mustapha Sule Lamido ya zo na biyu da kuri’u 368,726 sai kuma Aminu Ibrahim na NNPP ya zo na uku da Æ™uri’u 37,156.
Jihar Oyo
Tun kafin farko Hukumar zaÉ“e mai zaman kanta a Najeriya, INEC ta ayyana Seyi Makinde na Jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaÉ“en gwamna a jihar Oyo a zaÉ“en ranar Asabar da aka gudanar.
Makinde wanda shi ne gwamna mai ci a jihar ta Oyo ya samu Æ™uri’u mafi yawa inda ya bai wa babban É—an adawa a jihar, Teslim Folarin na Jam’iyyar APC tazarar Æ™uri’u dubu 300.
INEC ta ce Seyi Makinde ya samu Æ™uri’u 563,756 yayin da Teslim Folarin na APC ya samu Æ™uri’u 256,685.