Duniya na fuskantar barazanar karancin haihuwa a tsakanin ma’aurata – WHO

0
36

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta yi kiran a dauki matakin gaggawa kan magance ƙaruwar matsalar rashin haihuwa.

A wani sabon rahoto da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta fitar, ta ce sama da ɗaya bisa shida na baligai ne ke gaza samun haihuwa a wani mataki na rayuwarsu.

Daraktar fannin bincke kan lafiyar ma’aurata da haihuwa a hukumar, Pascale Allotey ta ce akwai ƙarancin kula da fannin rashin haihuwa.

WHO ta ce akwai buƙatar a gaggauta bijiro da hanyoyin samar da waraka ga matsalar rashin haihuwa tsakanin ma’aurata.

Sabon rahoton na cewa sama da ma’aurata guda cikin shida na fama da matsalar haihuwa a rayuwarsu.

Binciken ya kuma nuna rashin daidato tsakanin rukunin masu arziki da karamin karfi.

Pascale Allotey ta ce akwai ƙarancin kulawa kan batun haihuwa a wannan lokaci.

Ta ce adadin da ake samu na ma’aurata dake fama da matsalar haihuwa na nufin akwai damuwa, tare da buƙatar inganta hanyoyin tunkarar wannan matsala.

Da kuma gano musababbi da maganin matsalar.

A cewarta abu ne da kusan ba a bai wa fifiko da kyau, galibi mutane ba sa samun abin da suke so.

Hakan na nufin mutanen da ke neman taimako kan ƙare cikin uƙuba da kashe kuɗin da ya wuce kima.

Koda a ce wannan tsari akwai shi to ba kowa ke iya biya ba saboda tsadarsa.

Shugaban Hukumar lafiya ta dunya, Dakta Tedros Adhanom Ghabrayesus ya ce bincikensu ya huna musu cewa wannan ba matsalar da za a zura wa ido ba ne.

Ya kuma yi kira ga gwamnatocin ƙasashe da su riƙa bayar da fifiko domin masana su inganta bincike a kuma bijiro da tsare-tsare cikin sassauci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here