Kotu ta yankawa shararren mawakin Najeriya tikitin zaman gidan gyaran hali

0
23

Kotu ta aike da mawakin gambarar zamanin nan (Hip-hop) na Kudancin Najeriya, Habeeb Okikiola, wanda aka fi sani da Portable kurkuku, har zuwa lokacin da zai iya cika sharudan belinsa.

An dai gurfanar da Portable ne a gaban kotun majistare da ke Karamar Hukumar Ifo ta Jihar Ogun ranar Litinin, bisa zarginsa da cin zarafi.

Ana dai tuhumarsa ne da aikata laifuka biyar da suke da alaka da cin zarafi da kuma aikata sata da kuma kin amsa gayyatar ‘yan sanda.

Tun ranar Juma’a dai ake tsare da she bayan wani korafi da wani mai suna Osimusi Emmanuel ya shigar a kansa.

Sai dai bayan ya bayyana a gaban kotun ranar Juma’a, mawakin ya musanta aikata dukkan laifkuna da ake tuhumarsa da aikatawa.

Wani sashe na takardar tuhumar ya ce, “…cewa Insfekta Hammed Moshood da ASP Gregory Iyoha sun aike maka da takardar gayyatar ’yan sanda ranar 20 ga watan Janairun 2023 kan laifukan da ka aikata lokacin da suke kokarin aiwatar da aikinsu. Hakan laifi ne a sashe na 197 na kundin manyan laifuka na Jihar Ogun na shekara ta 2006.”

Sai dai lauyan Portable, Adodo Destiny, ya bukaci kotun da ta bayar da belin wanda yake karewa.

Da yake yanke hukunci, alkalin kotun, Mai Shari’a A.S. Soneye, ya bayar da Portable din beli a kan kudi N300,000, da kuma mutum biyu da za su tsaya masa da ke zaune a wajen da kotun ke da hurumi.

Sai dai alkalin ya aike da wanda ake tuhumar zuwa gidan gyaran hali na Ilaro, har zuwa lokacin da zia cika sharudan belin.

Ya kuma dage ci gaba da sauraron karar har zuwa 26 ga watan Afrilu domin fara shari’ar ka’in da na’in.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here