Shin Buhari ya cika alkawarin da ya daukarwa yan ‘yan Najeriya na sahihin zabe a 2023 ?

0
64

Gwamnatin Tarayya ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cika alkawarin da ya dauka na gudanar da sahihin zaben a 2023.

Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana hakan a birnin Washington DC a lokacin da yake ganawa da wasu kungiyoyin yada labarai na duniya.

Kamfanin Dillancin Labarai (NAN), ya ruwaito cewa ministan ya je Washington ne domin tattaunawa da kungiyoyin yada labarai na kasa da kasa da masu tunani kan zaben 2023 da aka kammala.

NAN ta kuma ruwaito cewa kawo yanzu ministan ya yi gana da “Washington Post”, Muryar Amurka, Associated Press da Mujallar manufofin kasashen waje.

Ministan ya ce Buhari ya cika alkawarin da ya yi na dawo da sahihin zabe, ya yanke shawarar cewa ba zai bai wa wata jam’iyyar siyasa dama ta musamman ba, ciki har da jam’iyyar APC mai mulki a lokacin zaben.

Ya ce a lokacin zabukan da suka gabata, shugaban kasar ya tabbatar da cewa babu wanda ya yi amfani da jami’an tsaro wajen magudin zabe amma ya samar da daidaito wajen gudanar da zaben.

“Misalin wannan alkawari, shi ne jam’iyyar shugaban kasa ta fadi zaben shugaban kasa a Katsina, jiharsa ta haihuwa.

“Haka zalika, zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, ya sha kaye a jiharsa ta Legas, yayin da shugaban jam’iyyar, Abdulahi Adamu, ya sha kaye a jihar Nasarawa a hannun jam’iyyar LP.

“Shugaban kungiyar yakin neman zaben jam’iyyarmu ma ya sha kaye a hannun PDP a Jihar Filato.

“Babu wani abu da ya ba wannan zaben ya koyar face gaskiya fiye, saboda babu wani magudi a jihohinmu,” in ji shi.

Ministan ya kara da cewa jam’iyyar APC ta sha kaye a jihohi hudu da suka fi yawan kuri’u a zabuka – Katsina, Kano, Kaduna da kuma Legas ko a lokacin da jam’iyyar ke rike da madafun iko.

Mohammed, ya ce zarge-zargen da ake yi na zamba da ‘yan adawa da masu zanga-zangar suka yi, bai taka kara ya karya ba.

A cewar ministan, rikicin ya samo asali ne saboda gazawar hukumar zabe ta INEC wajen dora sakamakon zaben shugaban kasa na ainihi a kan lokacin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here