Ohanaeze ta gindaya wa zababben shugaban Najeriya sharudda

0
64

Kungiyar ‘yan kabilar Igbo ta Ohanaeze, ta mika wa zababben shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu sharudda guda hudu, idan har yana bukatar goyon bayan ‘yan kabilar ta Igbo.

Babban sakataren kungiyar na kasar, Okechukwu Isiguzoro, ya ce daga cikin sharuddan da suka gindaya wa Tinubu, akwai bukatar ya sako Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar da ke rajin kafa ‘yantacciyar kasar Biafara ta IPOB.

Isiguzoro ya ce sako Kanu, daga gidan yari, zai taimaka sosai wajen wanzar da zaman lafiya a yankin Kudu maso Gabas.

Haka zalika kungiyar ta kuma ce, ya kamata Tinubu ya tabbatar da cewa an samar da shugaban majalisar dattijan kasar, daga yankin Kudu maso Gabas.

A cewar Ohaneze, ya kamata sabon zababben shugaban, da zarar ya karbi ragamar mulki, ya tabbatar da cewa an samar da jihohi akalla guda shida, daga yankin Kudu maso gabashin Najeriyar.

“Matsala guda daya tilo da tinubu yake da ita, ita ce yawan shekaru, amma mutanen da suka hana Buhari cika alkawuran da ya daukar wa ‘yan Najeriya, sune suke bibiyar sabon zababben shugaban a halin yanzu, don haka za su iya zzame masa babban kalubale” in ji Isiguzoro.

“Ya kamata Tinubu ya cika wa Kudu maso Gabas sharuddan da suka gindaya masa, idan har yana son ‘yan kabilar Igbo su mara masa baya.”

A cewar Isiguzoro, akwai bukatar zababben shugaban ya tabbatar da cewa, an samar da tsare-tsaren da za su habaka tattalin arzikin yankunan ‘yan kabilar Igbo, a kuma bude tashar jiragen ruwa ta Calabar, sannan a tsaftace kogin Azumiri da ke jihar Abia, hadi da yiwa ‘yan kungiyar IPOB afuwa, sannan kuma ya kamata ya biya diyya ga iyalan wadanda aka kashe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here