Yau Litinin ma’aikatan fannin sufurin jiragen sama a Najeriya za su fara yajin aikin kwanaki biyu, domin neman a kyautata musu yanayin aiki da kuma wasu kudade da suke bin gwamnati.
Tun a ranar Juma’ar da ta gabata, ma’aikatan sufurin saman suka sha alwashin tsunduma yajin aikin, wanda karo nan a biyu kenan da suke daukar irin matakin a shekarar bana.
Ma’aikatan da suka hada da matuka jirgin sama, da injiniyoyi da masu kula da zirga-zirgar jiragen saman a sararin samaniya, da dai sauran ma’aikatan filin jiragen, sun ce za su kaurace wa aiki ne a ranakun yau Litinin da gobe Talata bisa la’akari da basukan da suke bi, da kuma matakin gwamnati na rusa ofisoshin wasu hukumomin sufurin jiragen sama a Legas domin fadada filin jirgin saman birnin.
Fannin sufurin jiragen sama a Najeriya na fuskantar matsaloli da suka hada da rashin ingancin kayayyakin aiki a wasu filayen jiragen, da karancin mai da ke takaita zirga-zirgarsu a cikin gida, da kuma rashin isassun kudaden kasashen waje wanda ya sa kamfanonin jirage na kasa na kasa biyan wani kaso na kudaden da suka samu daga sayar da tikitinsu.