An kama limamin cocin da ya yaudari mabiyansa kan ganawa da Yesu

0
76

‘Yan sandan Kenya sun cafke Makenzie Nathenge, limamin cocin da ya janyo mutuwar wasu mabiyansa guda hudu, bayan da ya umarce su da kauracewa cin abinci domin a cewarsa hakan zai basu damar samun ganawa da Yesu Al Masihu cikin gaggawa.

Wasu karin mutane 11 jami’an tsaro suka samu nasarar cetowa daga halaka saboda yunwa a kusa da wani daji da ke gaf da garin Malindi a ranar Juma’ar da ta gabata.

‘Yan sanda sun ce dandazon mabiya ne suka yi sansani a gandun dajin, inda suka kwashe kwanaki da dama babu ci babu sha wai suna azumin jiran Yesu Al Masihu kamar yadda Faston yankin ya bukaci su yi.

Jami’an tsaron da ke cigaba da gudanar da bincike, sun ce akwai fargabar za a iya gano wasu karin mutanen da suka tagayyara ko ma suka sheka barzahu, a kokarinsu na bin umarnin limamin na su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here