Zaben Adamawa: INEC ta yi Allah wadai da cin zarafin da aka yi wa kwamishinanta

0
149

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta yi Allah-wadai da kakkausar murya dangane da cin zarafin kwamishinanta na kasa wanda aka yi masa tsirara, sakamakon ayyana wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Adamawa ba bisa ka’ida ba da kwamishinan zabe na jihar ya yi a ranar Lahadi.

Wani faifan bidiyo ya nuna cewa wasu da ba a san ko su waye ba sun yi wa kwamishinan INEC na kasa tsirara a jihar Adamawa

LEADERSHIP ta rahoto cewa, ga dukkan alamu, Matasan sun kama kwamishinan INEC na kasa ne bisa zargin cewa shine kwamishinan INEC na jiha, Ari Hudu (REC) wanda ya sanar da sakamakon zaben ba bisa ka’ida ba.

Da yake mayar da martani kan wannan lamari mai ban takaici, kwamishinan na kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu zabe, Barr. Festus Okoye, ya ce Hukumar ba za ta lamunci wannan cin zarafin ba.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here