Cutar Sankarau: Alamomi da hanyoyin magance ta

0
91

Cutar sankarau cuta ce da ke kashe jama’a da dama a fadin duniya.

Hukumar da ke yaki da cututtuka masu yaduwa ta Nijeriya NCDC ta bayyana cewa daga shekarar 2022 zuwa 2 ga watan Afrilun 2023, cutar ta sankarau ta kashe mutum 118 a jihohi 22 na kasar.

Haka kuma hukumar ta ce an samu mutum 1, 479 da suka kamu da cutar.

Hukumar da ke yaki da cututtuka masu yaduwa ta duniya CDC ta ce cutar tana barazana ga mutum miliyan 450 a kasashe 26 a nahiyar Afirka.

Mece ce sanakarau

Sanakarau dai wata cuta ce da ke kama mayafin da ke zagaye da kwakwalwa da lakka.

Akwai nau’o’in cutar sanakarau daban-daban, sai dai hukumar dakile cututtuka masu yaduwa ta Nijeriya ta bayyana cewa kwayoyin cutar da suka fi shahara wurin jawo sankarau sun hada da Neisseria da Haemophilus influenzae da kuma Streptococcus.

Haka kuma a cikin ukun nan sankarau din da aka fi kamuwa da ita, ita ce wadda kwayar cutar Neisseria ke jawowa.

Cutar ta sankarau dai ta fi kama kananan yara amma lokacin da ake annoba, tana kama har da manya.

Alamomin cutar sankarau

Hukumar NCDC ta bayyana cewa daga cikin alamomin cutar akwai ciwon kai da zazzabi da sankarewar wuya.

Haka kuma ta ce wanda ya kamu da cutar zai rinka gudun hasken fitila ko hasken rana haka kuma cutar tana kai ga har mutum ya suma.

Hukumar ta NCDC ta ce musamman ga yara kanana wadanda suka kamu da sankarau yana da wuya a ga wadannan alamomin, sai dai akasari yaran suna rashin walwala da kuma rashin cin abinci.

Haka kuma NCDC ta kara da cewa cutar dai tana iya sa mutum ya rinka amai da daukewar numfashi da kuma jinin mutum ya sauka.

Matakan kariya

Hukumar da ke yaki da cututtuka masu yaduwa ta duniya CDC ta bayyana cewa mataki mafi muhimmanci da mutum ya kamata ya soma dauka domin kiyaye kai daga kamuwa da sanakarau shi ne yin rigakafi.

Sauran matakan kariya daga cutar kamar yadda NCDC ta Nijeriya ta bayyana akwai kauce wa cunkoson jama’a sa’annan kuma a rinka tabbatarwa akwai isashen iska a cikin gida.

Hakan na nufin bude tagogi na da amfani domin samun isashen iska musamman da dare idan za a kwanta bacci.

Ganin cewa an fi samun sankarau a lokacin zafi, cunkusuwa a daki daya da babu isashen iska ma na taimakawa wurin kara yaduwar cutar.

Ga wasu daga cikin shawarwari da hukumar CDC ta bayar domin zama cikin koshin lafiya da kuma kare kai daga cututtuka irin sanakarau:

  • A rinka samun isashen hutu.
  • A daina matse wa marasa lafiya
  • Wanke hannu lokaci bayan lokaci da sabulu
  • A kuma rinka rufe baki da hanci da kyalle ko tolifefa idan za a yi tari ko kuma atishawa ( a rinka amfani da gwiwar hannu ko kuma gefen hannu idan babu kyalle).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here