Manchester City za ta fadada filin wasanta

0
72

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta mika takardun neman izinin fadada filin wasan ta na Eihad kan kudi fam miliyan 300 kuma za’a kara yawan kujerun zaman ‘yan kallo daga dubu hamsin da uku zuwa dubu sittin.

Cikin kare-karen da za ta yi wa filin har da wurin shaye-shaye a saman ginin da gyara fasalin rufin filin wasan da shaguna da wajen adana kayan tarihi sannan Manchester City za ta gina otal da zai dauki gadon kwanan mutun 400 da sauran tsare-tsaren da ta gabatar ga hukuma don neman izini.

Kungiyar ta ce aikin da zai kai shekara uku ana yi kan a kammala, zai samar da yanayi na cudanyar magoya baya da samar da nishadi da walwala, sannan kuma shirin zai lashe kudi fam miliyan 300 zai kuma samar da aiki ga mutum 2,600, za kuma ta bayar da fifiko ga mutanen Greater Manchester.

Haka kuma za’a gina ofisoshi domin bai wa masu kasuwanci haya, wadanda za su bunkasa kungiyar ta hanyar hadin gwiwa kamar yadda takardar neman izinin tayi bayani.

Tun cikin watan Agustan shekarar data gabata Manchester City ta sanar cewar ta fara tattaunawa kan yadda za ta fadada filin wasan ta na Etihad da wajen zaman ‘yan kallon kwallo.

An gina filin wasa na Ettihad ne a shekarar 2002 domin karbar bakuncin gasar Commonwealth Games daga nan ya koma wajen da Manchester City ke buga wasanninta a shekarar 2003.

A shekarar 2015 aka kara kujerun zaman ‘yan kallo zuwa dubu shida kawo yanzu filin wasan na Etihad shi ne na biyar a jerin filin da ke cin ‘yan kallo da yawa a Premier League ta Ingila.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here