Kamfanin sojojin haya na Wagner zai janye dakarunsa daga Ukraine

0
66

Shugaban kamfanin Wagner na kasar Rasha ya ce zai janye sojojinsa daga birnin Bakhmut na kasar Ukraine, a wani rikici da ya barke kan karancin makamai.

Bayanin nasa ya zo ne bayan da ya saka wani faifan bidiyo mai ban tausayi yana tafiya a cikin gawarwakin mayaka, inda ya nemi jami’an tsaro da su ba su karin kayayyaki.

Kasar Rasha dai ta shafe watanni tana kokarin kwace birnin duk da cewa akwai shakku akan dabarun da suke da shi.

Yevgeny Prigozhin ya yanke shawararsa kan halin da dakarunsa ke cciki na raashin makaman da za su kare kan su.

Ministan tsaron kasar Sergei Shoigu da babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Valery Gerasimov ne suka fi mayar da hankali kan fushin Prigozhin.

A makon da ya gabata ya shaidawa wani mai rajin kare yakin Rasha cewa mayakan Wagner a Bakhmut sun shiga wani hali a saboda rashin kayan aiki, don haka suna bukatar dubban harsasai.

Amma idan ba a magance karancin su ba, to za a tilasta wa sojojin haya ko dai su ja da baya ko kuma a rasa su,” in ji Prigozhin.

Ukraine ta yanke shawarar kare birnin ko ta halin kaka a wani yunkuri na mayar da hankali kan yadda zata lalata makaman sojojin Rasha.

Prigozhin ya ce dakarunsa sun amince su ci gaba da zama a Bakhmut har zuwa ranar 10 ga watan Mayu domin baiwa Rasha damar gudanar da bukukuwan ranar samun nasara a ranar Talata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here