Newcastle United na zawarcin Neymar, idanun Chelsea na kan Messi

0
50

Newcastle United na zawarcin dan wasan gaba na Brazil, mai taka leda a Paris St-Germain Neymar, mi shekara 31, a daidai lokacin da suke duba ‘yan wasan da za su saya a kaka mai zuwa.

Chelsea na sahun gaba a kungiyoyin da ke sin daukar dan wasan gaba na Lionel Messi, mai shekara 35, idan kwantiraginsa ya kare a PSG. (Football London)

Wolves sun yi wa Barcelona ta yin fam miliyan 30 kan dan wasan tsakiya na Portugal Ruben Neves, mai shekara 26, da kuma dan wasan tsakiya na Sifaniya Ansu Fati, dan shekara 20. (Relevo – in Spanish)

Barcelona ta karkata akalar zawarcin ta ga dan wasan tsakiya na Morocco Sofyan Amrabat, mai shekara 26, daga Fiorentina, wanda hakan ka iya karawa kungiyar Arsenal fatan dauko dan wasan tsakiya na Sifaniya Martin Zubimendi, 24, daga Real Sociedad.

Manchester United ta samu ci gaba a tattaunawa kan sabon kwantiragi kan mai kai hari na Ingila Marcus Rashford, mai shekara 25, inda suke fatan hada shi tare da dan wasan Tottenham kuam mai kai hari na Ingila Harry Kane, dan shekara 29.

Su kuwa Arsenal da Aston Villa na cikin kulub-kulub da ke zawarcin dan wasan Barcelona, kuma na tsakiyar Sifaniya Ferran Torres, 23. (Talksport)

Villa ma na duba yiuwuwar dauko dan wasan tsakiya na Sabiya, mai taka leda a Juventus Dusan Vlahovic, mai shekara 23, sannan su na zawarcin Torres. (Telegraph – subscription required)

Brighton ana da tabbacin tsohon dan wasan tsakiya na Ingila James Milner, mai shekara 37, zai dawo kungiyar, idan kwantiraginsa ya kare a Liverpool, wadanda suka fara shirin tayo dan wasan tsakiya na Argentina Alexis Mac Allister, mai shekaru 24, daga Seagulls. (Guardian)

Fulham za ta bukaci sama da fam miliyan 50 a wannan kakar, kan dan wasan tsakiya na Portugal Joao Palhinha, mai shekara 27, wanda ke hakilon taka leda a kungiyoyin Liverpool da Bayern Munich. (Football Insider)

Newcastle United ta shirya kan dan wasan tsakiya na Faransa mai shekaru 22 Khephren Thuram from Nice, wanda farashinsa shi ne fam miliyan 60, idan an bude kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa a duniyar tamaula . (Football Insider)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here