Za a yankewa Ekweremadu hukunci a Birtaniya

0
53
Wata kotu a birnin Landan za ta yankewa tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ike Ekweremadu hukunci bisa laifin safarar wani matashi da nufin cire kodarsa.

Za a yankewa tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya Ike Ekweremadu hukuncin ne bisa laifin safarar wani matashi da nufin cire kodarsa domin dasawa ‘yarsa da bata da lafiya a wani asibiti a Birtaniya.

Wata kotun ta Old Bailey da ke shari’ar manyan laifuka ta ce za a yanke masa hukuncin ne bisa laifin da ya sabawa dokokin Birtaniya na safarar sassan jikin dan adam.

Daga cikin wadanda za su fuskanci hukuncin, har da mai dakin Ekweremadu, Beatrice da kuma wani likita Obinna Obeta da ke da hannu wajen tsara aikata laifin.

A cikin makwannin da aka dauka ana gudanar da shari’ar, matashin mai shekaru 21 da aka dauko shi daga jihar Legas din Najeriya, ya tabbatar da cewa an kai shi Birtaniya ne da zumar cire masa koda bisa tukuicin kimanin Euro dubu 8, wanda bai fahimci hakan ba sai bayan da suka isa asibiti a Birtaniya.

Ana dai ganin tsohon dan majalisar na iya fuskantar hukuncin daurin rai da rai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here