Martanin Trump a kan hukuncin da kotu ta yanke masa bisa lalata da wata mata

0
47

Donald Trump dai ya mayar da martani a kan hukuncin, inda ya rubuta saƙonsa da manyan baƙaƙe a kafar sada zumuntarsa ta Truth.

“KWATA-KWATA BAN SAN MA WACE CE WANNAN MATAR BA. WANNAN HUKUNCI, ZUBAR DA MUTUNCI NE – CI GABA DA GAGARUMIN BI-TA-ƘULLI NE MAFI GIRMA A TSAWON ZAMANI!”, tsohon shugaban Amurkan ya ce.

Daga bisani, ɓangaren tsohon shugaban na Amurka ya fitar da wata sanarwa, wadda ta nanata iƙirarin da aka saba ji na cewa “bi-ta-da-ƙulli” ne a kan Donald Trump daga jam’iyyar Dimokrat.

“Kada a raba ɗaya biyu, ɗaukacin wannan shari’ar bogi, wani yunƙurin siyasa ne a kan Shugaba Trump saboda a yanzu shi ne gawurtaccen ɗan siyasar da ke kan gaba, kuma za a sake zaɓar sa Shugaban Amurka.”

“Ci gaba da tozarta gagarumin Tsarin Mulkinmu don cimma muradin siyasa abin ƙyama ne kuma ba za a lamunci hakan ba,” sanarwar ta ci gaba da faɗa.

“Ƙasarmu tana cikin gagarumar masifa, idan za a cika kotuna da jerin iƙirari, ba kuma tare da wata hujja ko shaida ko wanda ya gani ba, don samun maki a siyasance.”

Ɓangaren Trump ɗin ya kuma ce za su ɗaukaka ƙara kan wannan shari’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here