Kotun Bauchi ta tsare Dr. Idris kan zargin haddasa rikici

0
86

Hukumomi sun tsare malamin addinin Islama a Najeriya kuma babban limamin Masallacin Juma’a na Dutsen Tanshi, Dr. Idris Abdulaziz bisa zargin sa da ingiza tashin hankali tsakanin al’umma.

Lauyansa, Barista Umar Hassan ya shaida wa manema labarai cewa, wata kotun Majistire ce ta tsare malamin.

Hassan  ya ce, alkalin kotun ya hana bayar da belinsa, yayin da ya bada umarnin tsare shi kafin sake tasa keyarsa zuwa zauren kotun a gobe Talata.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, malamin ya mutunta gayyatar da jami’an ‘yan sanda suka yi masa kafin gurfanar da shi a gaban kotu.

A yayin gudanar da tafsirinsa na Al-Kur’ani a cikin watan azumin Ramadan, malamin ya furta wasu kalamai da wani bangare na Musulman kasar ya bayyana a matsayin rashin ladabi ga Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, lamarin da ya haddasa cece-kuce tsakanin malaman Najeriya.

Akwai dai wani bangare na malaman addinin Islama da ke goyon bayan sa, inda suke da fahimtar cewa, bai aikata laifi ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here