Liverpool ta kama hanyar samun gurbi a gasar zakarun Turai ta badi

0
64

Liverpool ta samu kwallayenta 3 ne ta hannun Curtis Jones a minti na 33 da 36 dukkaninsu da taimakon Mohamed Salah sai kuma kwallon Trent Alexandre-Arnold a minti na 71 shi ma dai da taimakon Salah.

Sai dai wannan nasara ba ta bayar da tabbacin yiwuwar Liverpool ta iya kai gurbin da take hari don samun tikitin gasar zakarun Turai domin kuwa yanzu ta na matsayin ta 5 ne da maki 65 tazarar maki 1 tsakaninta da Manchester United da kuma Newcastle wadanda kowannensu ke da wasa guda a hannu.

Nasara ko rashin nasarar kungiyoyin biyu a nan gaba ne zai fayyace makomar Liverpool wadda kuma ke fuskantar barazana daga Brighton wadda ke da wasa biyu a hannu, kuma yanzu haka ta na da maki 58 ne a matsayin ta 6.

Yayin wasan na jiya dai magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Leicester City sun rika ficewa daga filin wasa na Kings Power mintuna 20 gabanin kammala wasa bayan shan kayen kungiyar har gida da kwallaye 3 da nema, rashin nasarar da ke dakile fatanta na fita daga rukunin ‘yan dagaaji.

Duk da cewa Foxes za ta hadu da West Ham a wasan karshe da za ta doka cikin wannan kaka, amma rashin nasarar ta jiya ita ce babbar koma baya da ta dakushe yunkurinta na ganin ba ta tsinci kanta a Championship badi ba.

Idan har Everton ta yi nasara a wasanta da Wolves ranar asabar kai tsaye Leicester City za ta yi bankwana da gasar Firimiyar Ingila.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here