Maniyyatan da za su je hajji a jirgin farko sun yi hatsari

0
94

Maniyyatan aikin Hajjin bana daga Jihar Nasarawa da ke shirin tafiya a jirgin farko sun yi hatsari.

Rahotanni sun nuna mutum hudu sun samu rauni bayan motar maniyyatan ta yi adungure da su ne a ranar Laraba a kan hanyarsu ta zuwa Abuja inda za su hau farko a ranar Alhamis.

Hatsarin da ya ritsa da bas mai daukar mutum 18 da suke ciki ne a yankin Kara da ke Karamar Hukumar Keffi a Jihar Nasarawa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here