Majalisar dattawa ta amince da bukatar Tinubu ta nada mashawarta na musamman guda 20

0
87

Majalisar dattawa ta amince da bukatar shugaban kasa Bola Tinubu na nada masu ba shi shawara na musamman guda 20.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya karanta bukatar shugaban kasa a zauren majalisar a ranar Talata.

A cikin bukatar shugaban kasar bai bayyana sunayen mashawartan na musamman guda 20 ba.

Amma bayan karanta wasikar, majalisar dattawa ta amince da bukatar.

Hakan na zuwa ne bayan an rantsar da Tinubu a matsayin shugaban Najeriya na 16 a hukumance.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here