Chukkol ya maye gurbin Bawa a matsayin shugaban EFCC na rikon kwarya

0
85

Daraktan Ayyuka a Hukumar Yaki da Masu Yi Wa Tattalin Arziki Zagon Kasa (EFCC) Abdulkarim Chukkol ya zama mukaddashin Shugaban hukumar.

Aminiya ta rawaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Abdulrasheed Bawa daga matsayin shugaban hukumar ranar Laraba don yin bincike a kansa.

Wata sanarwa mai dauke da sa hannun Daraktan Yada Labarai a ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Willie Bassey ta umarci Bawa da ya mika wa Daraktan ragamar hukumar ba tare da bata lokaci ba.

Bincike ya nuna Abdulkarim Chukkol, wanda babban jami’in bincike ne a hukumar, zai ci gaba da jan ragamar hukumar har zuwa lokacin da za a nada sabon shugaba.

Chukkol ya yi digiri na farko a fannin Kimiyya a Jami’ar Maiduguri a 2000, sannan ya yi karatun Difloma a fannin Shari’a a Jami’ar Virginia da ke kasar Amurka a 2011.

Dan sanda ne wanda ya shiga hukumar EFCC a shekara ta 2003 kuma ya kai matsayin babban jami’in bincike kuma daraktan ayyuka.

Ya taba zama a makarantar horar da jami’an FBI, wato Quantico.

Chukkol ya taba yin shugabancin ofishin shiyya na Fatakwal na hukumar kafin daga bisani aka mayar da shi hedikwatar hukumar da ke Abuja.

Daga nan ya karbi ragamar aiki daga hannun Mohammed Abba a matsayin Daraktan Ayyuka, wanda ya koma Rundunar ’Yan Sandan Najeriya bayan ya rike mukamin mukaddashin shugaban hukumar bayan dakatar da Magu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here