An bai wa iyalan ‘yan sandan da suka mutu a bakin aiki cakin Naira miliyan 23 a Zamfara

0
89

Kwamishinan ‘yansandan jihar Zamfara, Muhammad Bunu, a madadin babban sufeton ‘yan sanda na kasa, Usman Alkali Baba ya gabatar da cakin kudi miliyan 23,574,204 ga iyalai da ‘yan uwa 21 na jami’an ‘yan sanda da suka rasa rayukansu a bakin aiki.

Kakakin ‘yansandan Jihar, ASP Yazid Abubakar, ya bayyana haka a takardar da ya sa wa hannu ga manema labarai a Gusau.

A cewarsa, Kwamishina Bunu, a lokacin da yake gabatar da cakin, ya yaba wa Sufeton ‘yansandan bisa irin wannan karimcin da ya nuna, sannan kuma ya bukaci iyalan jami’an da suka mutu da su yi amfani da kudaden wajen kula da iyalansu cikin adalci.

Abdulrahman Ahmed, daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin a jawabinsa a madadin sauran wadanda suka amfana, ya mika godiyarsa ga Sufeto Janar na ‘yansanda da kuma rundunar ‘yansanda bisa tallafin da suka ba su, ya kuma ba da tabbacin cewa za a kashe kudaden da aka ba su ta hanyar da ta dace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here