Fatan da ya rage na warware rikicin juyin mulkin Nijar

0
140

Kasashen Yammacin Afirka da manyan kasashen duniya suna fatan samun wata dama ta yin sulhu da sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar kafin taron da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka, ECOWAS za ta yi ranar Alhamis.

ECOWAS ta sanar cewa shugabanninta za su sake ganawa a Abuja domin tattaunawa kan halin da ake ciki a Nijar bayan wa’adin da ta bai wa sojoji na mayar da Mohamed Bazoum kan mulki ya cika ba tare da sun yi biyayya ga umarnin ba.

Kungiyar ta sha alwashin yin amfani da karfin soji kan sojojin da suka yi juyin mulki bayan da ta kakaba musu takunkumai da suka hada da na tattalin arziki da rufe iyakokinsu da kasar da kuma katse wutar lantarki.

Sai dai sojojin sun yi alkwarin mayar da martani “mai karfi kuma cikin gaggawa” kan duk wani kutse da za a yi musu daga kasashen waje.

“Babu shakka diflomasiyya ita ce hanyar da ta fi dacewa ta warware wannan matsala,” a cewar Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken a hirarsa da gidan rediyon RFI ranar Talata.

Ya kara da cewa Amurka tana goyon bayan yunkurin da ECOWAS take yi na maido da tsarin mulki a Nijar.

Sai dai ya ki yin tsokaci game da makomar sojojin Amurka 1,100 da ke jibge a Nijar.

Ranar Litinin Mataimakiyarsa ta gana da manyan jami’ai na sojojin da suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum ba tare da samun wani kwarin gwiwar warware matsalar ba.

Victoria Nuland ta ce ba a bar ta ta gana da jagoran juyin mulki Abdourahamane Tchiani da kuma hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum ba.

Sai dai ta hadu da mutumin da ya bayyana kansa a matsayin shugaban rundunar tsaro ta sojojin da suka yi juyin mulki, Moussa Salaou Barmou da kanar-kanar guda uku.

Ta kara da cewa ba a samu ci-gaba a ganawa “mai wahala” da ta yi da sojojin ba.

Hasalima ta kai ziyarar ce a yayin da sojojin suka nada tsohon Ministan Kudi na kasar Ali Mahamane Lamine Zeine a matsayin sabon Firaiminista.

A nata bangaren, gwamnatin Jamus ta gargadi sojojin da kada su kuskura su yi Shugaba Mohamed Bazoum da iyalansa illa.

“Hakan ne ya sa nake son yin amfani da wannan dama na kara aikewa da sako ga sojojin da suka yi juyin mulki cewa za su dandana kudarsu idan wani abu ya faru da zababben shugaba Bazoum da iyalansa,” in ji kakakin Ma’aikatar Wajen kasar Sebastian Fischer, a hirarsa da ‘yan jarida a Berlin ranar Litinin.

Sai dai Mali da Burkina Faso sun ce za su tura wakilai Jamhuriyar Nijar ranar Litinin domin nuna goyon baya ga sojojin da suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum.

“Manufar hakan ita ce mu muna goyon bayan mu kasashe biyu ga ‘yar uwarmu Nijar,” a cewar wata sanarwa da rundunar sojin Mali ta fitar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here