Tinubu ya sake kakaba wa Nijar takunkumai

0
140

Shugaban Ecowas, Bola Tinubu, ya umarci Babban Bankin Najeriya ya sanya ƙarin takunkuman kuɗi a kan hukumomi da ɗaiɗaikun mutanen da ke da alaƙa da shugabannin juyin mulki a Nijar. 

Wata sanarwa da mai bai wa shugaban na Najeriya shawara na musamman kan harkar yaɗa labarai, Anjuri Ngalale ta ce Tinubu ya umarci gwamnan babban bankin na CBN ya ƙaƙaba wasu jerin takunkumai a kan masu hulɗa da sojojin da ke mulkin Nijar. 

Matakin na zuwa bayan ƙarewar wa’adin mako ɗaya da ƙungiyar Ecowas ta bai wa sojojin Nijar bisa tanadin yarjejeniyar sanya takunkuman kuɗi na shugabannin ƙasashen ƙungiyar Ecowas. 

Shugaba Tinubu ya ce bai ɗauki matakin cikin kuskure ba ne, saboda ya samu izini daga takwarorinsa na Ecowas don fitar da sanarwa, ya kuma nanata cewa matsayin, ba al’amari ne da ya ɗauka da sunan wani shugaban ƙasa guda ɗaya ba. 

Ya ce takunkuman da aka sanya wa Nijar, mataki ne da ya ɗauka a matsayinsa na shugaban Ecowas, kuma shugaban Najeriya, amma yana tsaye a kan ikon da yarjejeniyar ƙudurin dukkan ƙasashe wakilan Ecowas da shugabannin ƙasashen ƙungiyar. 

A cewarsa, matakin iko ne, da ba na gwamnatin Najeriya ba, ƙuduri ne da aka zartar a bainar jama’a kafin wannan lokaci. Shugaban Najeriyar dai yana mayar martani ne ga sukar da yake fuskanta a ciki da wajen ƙasar game da matakin sanya wa Nijar takunkumai da barazanar ɗaukar matakin soji na ƙungiyar Ecowas, bayan hamɓarar da Shugaba Mohamed Bazoum daga mulki. 

Tinubu ya ce bayar da wa’adi ga Nijar, hurumin Ecowas ne, ba na Najeriya ba. 

A cewarsa Najeriya, ba ta bai wa Nijar wani wa’adi ba. Sanarwar ta kuma ambato shugaban Najeriyar na cewa a ‘yan kwanakin nan, bayan cikar wa’adin Ecowas, ya faɗada tuntuɓa a ciki da wajen ƙasar ciki har da musayar ra’ayi da gwamnonin jihohi masu iyaka da Nijar dangane da abin da ya faru a maƙwabciyar ƙasar. 

Amma Shugaba Tinubu ya nanata ƙudurin cewa duk martanin da Ecowas ta mayar da kuma wanda za ta mayar a kan batun juyin mulkin Nijar, zai kasance ne ba tare da la’akari ko tunanin bambancin ƙabila ko addini ba. 

Ya ce ƙungiyar ta ƙunshi dukkan ƙabilu da addinai daban-daban da kuma sauran nau’o’in bambance-bambancen al’ummomin Afirka ta Yamma, don haka martanin Ecowas zai kasance ya yi la’akari da duk waɗannan ɓangarori, amma ba wani daga cikinsu ba. 

Ya ce duk da yake babu wani zaɓi da aka ɗauke a jerin matakan da za a iya amfani da su, ƙungiyar za ta gudanar da taron ƙoli a Abuja ranar Alhamis, inda ake sa rai Ecowas za ta cimma muhimman shawarwari a kan matakai na gaba a kan Nijar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here