WAEC ta rike sakamakon jarrabawar dalibai 262,803

0
112

Hukumar shirya jarrabawar ƙasashen yammacin Afrika (WAEC) ta riƙe sakamakon jarrabawar ɗalibai 262,803 da suka rubuta jarrabawar kammala babbar sakandare ta 2023. 

Shugaban ofishin hukumar a Legas, Patrick Areghan, ya ce an rike sakamakon jarrabawar ne bayan samun dalibai da tafka maguɗi a matakai daban-daban na jarabawar.

Ya ce kashi 16.29 na jimillar ɗaliban da suka rubuta jarrabawar ne lamarin ya shafa. 

Mista Areghan ya yi bayanin cewa “dailan samun irin wannan matsala a bayyane suke, ɗalibai ba su zage damtse suka yi karatu ba, inda suka dogara da satar amsa a yayin jarrabawa.”

Ya ƙara da cewa ɗaliban da lamarin ya shafa suna da zaɓin gabatar da kansu don bincike da kuma neman damar wanke kansu daga wannan zargi na tafka maguɗin jarabawar, kamar yadda aka saba yi a baya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here