Zargin cin hanci ya yi wa kotun zaben Kano dabaibayi

0
107


Dambarwa ta ɓarke, bayan Mai shari’a Flora Ngozi Azinge, shugabar kotun sauraron ƙorafin zaɓen ‘yan majalisun tarayya da na jihar Kano, ta sake fitowa ta koka game da yunƙurin bai wa alƙalan kotun cin hanci da nufin tauye adalci.

Manyan jam’iyyun siyasar jihar guda biyu NNPP mai mulki da APC, babbar mai hamayya a Kano suna nuna wa juna yatsa.

Rahotanni dai sun ambato Mai shari’a Flora Azinge na cewa karo na biyu kenan wani alƙalin kotun na kai mata ƙorafi a kan yadda wasu lauyoyi da ke cikin ƙararrakin da kotun ke sauraro, suna ƙoƙarin ba su cin hanci.

Zargin na babbar alƙaliyar, na nuna tsananin rufewar idon ‘yan siyasa, ta yadda wasu ke ƙoƙarin sayen nasarar da suka kasa samu ta halastacciyar hanya daga jama’ar da za su mulka ba.
Ba a saba jin wani alƙali ko wata alƙaliya sun fito bainar jama’a suna kokawa a kan ƙoƙarin ba su toshiyar baki ko cin hanci a Najeriya ba.

Sai dai kamar yadda aka saba, a wannan karo ma, duk manyan masu ruwa da tsaki sun fito bainar jama’a suna tsame kansu daga zargin da mai shari’ar ta yi.

Gwamnatin jihar ta Kano ce dai ta fara fitowa tana nesanta kanta, sai dai ba ta tsaya a nan ba, ta riƙa yin ishara da sashen takwararta mai adawa wato APC.
Amma su ma ‘yan adawar na Kano, APC sun sa ƙafa sun yi watsi da wannan al’amari, sun ma ƙara da zargin gwamnatin NNPP da yunƙurin ɓata sunan jam’iyyar tasu da ma na mai shari’ar.

Zarge-zargen ba da cin hanci ga alƙalan dai ga alama ya damu, ƙungiyar lauyoyi ta Kano, wadda shugabanta na jihar, Barista Sagir Sulaiman Gezawa ya rubuta wata wasiƙa ga kotun, yana neman ta bayyana sunayen lauyoyin da suka yi yunƙurin bai wa alƙalai toshiyar baki.

Ya dai ce za su gudanar da bincike don sanin irin matakin ladabtarwa da za su iya ɗauka a kan masu yunƙurin ba da cin hanci da kuma ganin yadda za su kai lauyoyin da ake zargi gaba.

Ya kuma ce tuni sun aika kwafin wasiƙa ga majalisar alƙalai ta ƙasa da shugabar kotun ɗaukaka ƙara da kuma shugaban ƙungiyar lauyoyi na Najeriya a kan batun.

A cewarsa, ƙungiyar da yake jagoranta ta kuma nemi ganawa da alƙalan kotun zaɓen ta Kano, sannan ya nanata alƙawarin ƙungiyarsa ga yaƙi da cin hanci da rashawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here