Gwamnatin tarayya za ta bai wa kowacce jiha naira biliyan biyar don rage radadi

0
114
Tinubu
Tinubu

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta amince da bai wa kowacce jihar naira biliyan biyar domin sayen kayan abinci don raba wa talakawa a jihohin a matsayin kayan rage raÉ—aÉ—i.

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim – kaÉ—an bayan kammala taron majalisar tattalin arziki da aka gudanar a fadar gwamnatin Æ™asar da ke Abuja.

Matakin na zuwa ne mako guda bayan tashin gwauron zabi da farashin kayan abinci suka yi a ƙasar da kusan kashi fiye da 20 cikin 100 cikin shekara 18.

Lamarin da masana ke dangantawa da cire tallafin man fetur da gwamnatin ƙasar ta yi.

Gwamnan na jihar Borno ya ce gwamnatin tarayya ta bai wa kowane gwamna tirela biyar na shinkafa domin rabawa a jiharsa.

Zulum ya ce gwamnonin za su sayi buhun shinkafa 100,000 da na masara 40,000 da kuma takin zamani domin raba wa al’umominsu do taimaka musu wajen rage raÉ—aÉ—in tsadar rayuwa da suke fuskanta.

Tun da farko sakataren gwamnatin tarayya George Akume ya ce an bai wa jihohin ƙasar 36 tirela 100 na taki da tirela 100 ma hatsi a matsayin tallafin rage raɗaɗin.

Mista Akume ya bayyana hakan ne a lokacin bikin ƙaddamar da littafin tarihin Edwin Clark.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here