Ana yi wa Donald Trump barazanar daurin shekaru da dama kan zarginsa da laifuka 78

0
178

Ana zargin Donald Trump da tuhume-tuhume 78 inda yake gaban kotu a yanzu. Shin ta yaya zai iya kare kansa da kuma samun nasara kan zarge-zarge guda uku da ake ƙararsa a kai?

Ana zargin tsohon shugaban Amurkar da aikata jerin laifuka, da suka kunshi haɗa baki don sauya sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na 2020 wanda hakan tauye ƴancin Amurkawa ne na yin zaɓe.

Sauran sun haÉ—a da É“oye takardu na wasu kadarorinsa guda biyu, da amfani da kuma biyan tauraruwar fina-finan batsa kuÉ—i domin ta É“oye mu’amalr da suka yi gabanin zaÉ“en Æ™asar a 2016.

Yana fuskantar zarge-zarge kusan 80 a jihohi guda uku ko ma fiye da haka, saboda an tuhume shi da sanya baki a zaɓen jihar Georgia.

Mun ga yadda tuhumar da ake yi wa Trump ke gudana – amma ta yaya zai iya kare kansa a zaman fara sauraron shari’arsa a shekara mai zuwa bayan musanta aikata tuhume-tuhumen?

Shin zai iya samun nasara cikin sauki?

Cikin tuhumar da ake yi wa Trump, akwai har da batun É“oye takardu na Florida, kamar yadda wani masanin shari’a ya faÉ—a wa BBC.

“Yayin da batun zai iya zama babbar tuhuma – masu taya alkali shari’a za su iya yin duk mai yiwuwa ko samun wani mai taya alkali shari’a domin wanke Donald Trump daga tuhumar da ake yi masa,” a cewar Anthony Michael Kries, wani farfesa a fannin zaÉ“e a Jami’ar Jihar Georgia.

Sashin shari’a ya zargi Trump da É—aukar wasu takardu masu muhimmanci daga Fadar White House bayan barinsa ofis, inda ya kai su wani rukunin gidansa da kin bai wa gwamnati haÉ—in kai wajen Æ™wato takardun.

Dokokin Amurka sun buƙaci shugaban ƙasa da ya miƙa irin waɗannan takardu zuwa ga hukumar adana takardu da kayayyakin tarihi na ƙasar.

Haka nan ma, dokar ta buƙaci tsoffin masu riƙe da ofisoshi, kamar tsohon mataimakin shugaban ƙasar Mike Pence, su dawo da takardun da zarar sun same su.

An gabatar da tarihin hujjoji a kan zargin da ake yi wa Mista Trump, wanda ya haɗa da hotunan akwatuna da aka ɓoye a gidansa na Florida. Masu shigar da ƙara sun samu wani sautin murya na Mista Trump yana magana kan wasu takardun sirri a gaban mutane, inda ya ce ba zai ci gaba da ɗaukarsu a matsayin takardun sirri ba tun da ya bar ofis.

Mista Trump ya yi kuskuren iÆ™irari a bainar jama’a cewa ba zai ci gaba da É—aukar takardun a matsayin na sirri ba. Ya musanta aikata laifi bayan gurfanar da shi a gaban kotu a birnin Miami a watan Yuni, inda ya kira Æ™arar da cewa tana da alaÆ™a da siyasa.

Sai dai zai iya samun taimako a wajen masu taimaka taya alkali shari’a. Mista Trump yana da masoya da maÆ™iya a kudancin Florida kuma masana shari”a a can sun ce zaÉ“ar masu taya alkali shari’a da ba su da bambanci zai zama da wahala.

“Cikin masu taya alkalin akwai masu manufofi daban-daban,” kamar yadda Rob Mendell, wani babban alkali a Florida ya faÉ—a wa BBC a watan Yuni.

Shari’a mai matuÆ™ar tangal-tangal

Shari’a ta farko da Mista Trump ya fuskanta a wannan shekara za ta iya zama wadda zai iya samun nasara ba tare da ya sha wahala ba.

A watan Maris, masu gabatar da ƙara a New York suka gabatar da tuhume-tuhumen laifi 34 na yin ƙarya a ɓangaren kasuwanci. Akwai kuma zargin da ake yi wa lauyan Mista Trump na bai wa wata mai fim ɗin batsa toshiyar baki na $130,000 a makonnin karshe na yakin neman zaɓen 2016.

KuÉ—in da aka bai wa matar shi ne domin dakatar da ita faÉ—ar cewa tayi mu’amala da tsohon shugaban na Amurka, abu kuma da ya musanta.

Wani babban alkali a birnin Manhattan Alvin Bragg ya yi zargin cewa Trump ya biya kuÉ—in ne ta hannun lauyansa, Michael Cohen, inda ya rubuta cewa kuÉ—i ne da aka kashe a matsayin shari’a.

A wani taron manema labarai da Mista Bragg ya yi a watan Afrilu, ya yi zargin cewa Trump ya biya kuɗaɗen ne domin toshe laifukan da ya aikata waɗanda ke da alaƙa da zaɓen 2016, da kuma saɓa wa biyan kuɗin haraji.

Tawagar Mista Trump sun yi yunkurin sauya wurin shari’ar daga jiha zuwa kotun tarayya da kuma Æ™oÆ™arin ganin an kori Æ™arar. Sun sha kalubalantar masu zargin cewa Trump ya biya kuÉ—in ne don kada iyalinsa su ji kunya, ba wai aikata laifi.

Wani mataki da wani babban alkali ya yanke na hana Trump mayar da shari’ar zuwa tarayya a watan Yuli, babbar nasara ce a garemu,” in ji Mista Bragg yayin tattaunawa da wani gidan rediyo a wannan mako.

‘Shari’ar da za ta yi wa Trump wuyar tsallakewa’

A makon da ya gabata, Sashin Shari’a ya zargi Mista Trump kan tuhume-tuhume guda huÉ—u da suka shafi maguÉ—in zaÉ“e. Zargi ne da ba a taÉ“a ganin an yi wa wani shugaban Æ™asa ba na Æ™oÆ™arin amfani da karfin don yin kane-kane a kan mulki.

An kuma zarge shi da matsawa jami’an zaÉ“e da mataimakin shugaban Æ™asa don sauya sakamakon zaÉ“en 2020, zaÉ“en da ya sha kaye a hannun Joe Biden.

An kuma zarge shi da yaɗa labaran ƙarya cewa an sace zaɓen, wanda ya janyo tayar da tarzoma a Majalisar Dokokin Ƙasar ta Amurka.

Wasu masana shari’a na tunanin cewa irin jerin hujjoji da ake da su, da aiki ba sani ba sabo na tsarin shari’ar Washigton DC, da kuma yadda lauya na musaman Jack Smith ya tsara Æ™arar, na nufin cewa Trump yana da babban kalubale a gabansa.

“Tarzomar siyasa a DC – ina ganin batu ne mai matukar tangal-tangal,” a cewar Mista Kreis. “Ina ganin hakan zai iya zamanto masa abu ne mai wahala ya tsallake.”

Wani abu da Mista Trump zai fi kalubalanta shi ne cewa ko ya yi niyyar aikata waɗannan laifuka. A yanzu sai masu shigar da ƙara sun nuna cewa Trump ya yi karya a lokacin aikata laifukan.

Mista Kreis ya ce abu mafi muhimmanci shi ne “Shin Trump ya amince cewa an tafka maguÉ—i a zaÉ“en Amurka sannan ya tabbatar shi ya ci zaÉ“en?”.

Lauyan Mista Trump John Lauro ya ce tsohon shugaban Æ™asar ya yi imanin cewa shi ya ci zaÉ“en kuma sakamakon shari’ar ba zai bayyana wani abu saÉ“anin haka ba.

Masu taya alkali shari’a da ke da zafin rai

Ko ta yaya duka É“angarorin suka kalubalanci shari’ar, sai sun tabbatar wa da alkali cewa suna da gaskiya. Kuma wannan abu ne mai matukar yin hasashen sakamakon shari’a, in ji masana shari’a.

Hukunce-hukunce daban-daban guda huÉ—u – kama daga Washington DC, Florida, Manhattan da yiwuwar Georgia – za su haifar da ra’ayoyi huÉ—u daban-daban daga wajen alkalai.

“Hakan zai kawo sauki ga lamarin Trump,” in ji Mista Kreis. “Ba ya buÆ™atar ya shawo kan mutane 12… mutum É—aya kawai suke bukata.”

Wani babban canjin shi ne Mista Trump da kansa.

A ra’ayinsa zai iya jinkirta duk wani hukunci ta hanyar É—aukaka Æ™ara, idan ya lashe zaÉ“en shugaban Æ™asa, zai iya matsa wa Ma’aikatar Shari’a ta janye bincikenta.

Ko ma, kamar yadda aka ruwaito a baya, ya gafarta wa kansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here