‘Yan Najeriya miliyan 18 na cikin tsananin yunwa – Rahoto

0
107

Jaridar leadership da ake wallafawa a Najeriya ta rawaito cewa masu ruwa da tsaki a bangaren noma a kasar sun ci gaba da bayyana damuwarsu a kan yadda ake garkuwa da manoma, abin da ke illa ga bangaren samar da abinci a kasar.

Wani bincike da jaridar leadership ta gudnar na nuna yawan ‘yan Najeriya da ke fama da matsalar rashin abinci tsakanin rubu’in farko na shekarar bara zuwa rubu’in farko na bana, ya karu daga miliyan 66 da dubu 200 zuwa miliyan 100.

Binciken ya kuma ce, daga  cikinsu, akalla mutane miliyan 18 da dubu 600 ke fama da matsananciyar yunwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here