Zan shawo kan matsalar hauhawar farashi nan ba da jimawa ba – Tinubu

0
99

Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar wa ƴan Najeriya cewa gwamnatinsa za ta shawo kan matsalar taɓarɓarewar tattalin arziki da kasar ke fama da shi, ciki har da sauko da hauhawar farashin kayayyaki.

Ya ce duk da cewa shi ba na daban bane, amma kada ‘yan Najeriya su damu saboda yana da zimmar kawo karshen hauhawar farashi.

Tinubu ya bayyana haka ne lokacin da ya karɓi bakuncin kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC a wajen buɗe-baki a fadarsa da ke Abuja ranar Laraba, inda ya ce gwamnatinsa na aiki tukuru don sauko da farashin kayayyaki.

“Wannan alkawari ne mai wahala da kuka yi wa al’ummar Najeriya lokacin da kuke min yakin neman zaɓe, dole ne na yi aiki don tabbatar da haka.

“Na yi kamfe kan fata mai kyau, dole ne na ɗabbaka wannan fata da kuma fatan ganin kowaye cikinmu ya ji daɗi. Tattalin arzikinmu na kan turba mai kyau. Kada ku damu kan haka,” in ji Tinubu.

Ya ce Najeriya na fama da matsalar hauhawar farashi kuma a shirye gwamnatinsa take wajen magance ta.

“Muna sake fasalin harkokin kuɗir shigarmu, kuma muna samun nasara kan haka, kuma muna dawo da tagomashinmu a faɗin duniya,” in ji shugaban Najeriyar.

“Muna sake fasalin harkokin kuɗir shigarmu, kuma muna samun nasara kan haka, kuma muna dawo da tagomashinmu a faɗin duniya,” in ji shugaba Tinubu.

BBC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here