Yan ta’adda sun sace mata da kananan yara a Katsina

0
160

Yan bindiga sun kai samame a garin Na-Alma a yankin karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina , inda suka kona gidaje, suka kuma sace gomman mutane, galibi mata, har da masu juna biyu, da kananan yara, da wani wanda ‘yan bindiga suka taba sare wa hannu da kafa, bayan kashe wani mai unguwa.

Bayanai sun ce, hare-haren ‘yan bindigan na baya-bayan nan sun jefa mutane da dama cikin tasku.

Wani mutumin yankin, wanda ya tsallake rijiya da kundun baya ya ce suna cikin rudani, kuma kashi takwas cikin goma na mutanen garin sun yi kaura.

Mutumin ya kuma ce sun shaida wa jami’an tsaro cewa sun samu bayanan sirri na harin da ƴanbindigar za su kai garin nasu : ” Tun wajen takwas da rabi na dare muka shaida wa jami’an tsaro amman ba su zo ba har sai da mutanennan suka shiga suka fara harbi, sai dai kawai su ce ga su nan zuwa, amman ba su zo ba har sai da ƴanbindiga suka gama kone-kone da duk abin da za su yi sannan suka zo.”

Mutumin ya kara da cewa an yi masu gagarumin ta’adi a harin da ‘yanbindigan suka kai “Asarar kam Allah kadai Ya san yawanta saboda haka suka bi gida-gida suka ƙona kuma duk manyan gidaje ne suka kona sun kuma kashe mai-unguwa.”

Mutumin da muka sakaya sunansa ya ce maharan sun tafi da wani Alhaji da suka datse wa ƙafa da hannu kwanakin baya, sannan mata sun kai tara wadanda kowace na da goyo da kuma wasu masu ciki biyu, ” Idan aka hada da matan da yaran da wannan Alhajin za su kai mutum 20.”

Mutanen yankin sun ce suna fuskantar hare-haren ƴanbindiga fiye da kowane lokaci.

Kwamishinan tsaro na jihar Katsina, Dakta Nasiru Mu’azu ya danganta wannan hari da aka kai garin Na-Alma, da cewa hari ne irin na ramuwar gayya.

Sakamakon halaka wani mutum da ake zargin kasurgumin dan bindiga ne da mukarrabansa, wadanda suka addabi yankin karamar hukumar Malumfashi da kewayenta. 

Kuma ana nan ana ci gaba da kokarin murkushe wannan matsala ta tsaro a dukkan wuraren da ake fama da ita a jihar ta Katsina, in ji shi.

BBC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here