Jamus ta kama yan Najeriya da ake zargin yan kungiyar asiri ne

0
93

Ƴan sandan Jamus sun kama ƴan Najeriya 11 da ake zargin ƴan ƙungiyar asiri ne da suke shirya soyayyar ƙarya don yaudara.

A wata sanarwa da ƴan sandan Bavarian suka fitar, ƴan ƙungiyar asirin ta Black Axe sun aikata manyan laifuka da dama a faɗin duniya.

Ƴan sandan sun ƙara da cewa ƙungiyar ta mayar da hankali kan ƙulla soyayyar ƙarya da kuma halasta kuɗin haram a Jamus.

Sanarwar ta ce, “suna yin ɓadda kama, misali suna nuna zuwa da niyyar aure sannan bayan jan ɗan lokaci ana soyayyar sai su nemi a basu kuɗaɗen yin wasu ɓukatu”.

Ɓangarorin da ƙungiyar take aiki a faɗin duniya sun haɗa da ” safarar bil’adama da yaudara da halasta kuɗin haram da safarar miyagun ƙwayoyi”.

Waɗanda aka kama ɗin duka ƴan Najeriya ne kuma ƴan shekaru tsakanin 29 da 53.

An tsare su a ranar Talata a sumamen da aka kai yankin Bavaria bayan binciken ƴan sanda da aka shafe sama da shekara biyu ana yi.

Wani binciken BBC da aka ƙaddamar a 2021 kan ƙungiyar asiri ta Black Axe ya zaƙulo shedu da suke nuna ƙungiyar ta shiga harkar siyasa a Najeriya kuma tana aiwatar da kashe-kashe a faɗin duniya.

BBC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here