Yadda matsalar man fetur ta ‘rincabe’ a sassan Najeriya

0
158
man fetur
man fetur

Al’umma na ci gaba da fuskantar matsalar ƙarancin mai a faɗin Najeriya abin da ya sa masu sayar da man a kasuwar bayan fage ke cin karensu babu babbaka inda har suke sayar da shi kan N1,200 duk lita ɗaya a wasu yankunan.

Tun makon da ya gabata ake ganin dogayen layuka na ababen hawa a gidajen man da ke sayarwa, yayin da wasu kuma suke kulle saboda ba sa sayarwa.

Lamarin na zuwa ne yayin da a baya-bayan nan kamfanin mai na Najeriya, NNPCL ya ce ya magance matsalar da ke janyo ƙarancin man.

Ita ma ƙungiyar dillalan man fetur da Iskar Gas ta arewacin Najeriya, AROGMA, ta ce akwai wasu tarin matsalolin da suka assasa yanayi da ake ciki, kuma ya zama dole a lalubon bakin zarensu.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a Abuja, babban birnin Najeriya da wasu jihohi, gidajen mai sun ƙara kuɗi inda suke sayar da shi tsakanin N750 da N800 kowace lita ɗaya.

A gidajen man NNPCL da suke sayar da shi kan N617 kowace lita ɗaya, sai dai akwai dogayen layukan ababen hawa.

A jihar Jigawa kuma, an rufe gidajen mai da dama inda ƴan bumburutu ke sayar da man a kan N1,100 kowace lita ɗaya.

A wasu yankunan jihar Legas kuwa, masu sayar da man a kasuwar bayen fage na saida lita biyar ta mai a kan N5,500.

Akasarin gidajen mai a Alimosho da Ojo da ƙaramar hukumar Badagry a rufe suke sannan akwai dogayen layukan ababen hawa a gidajen mai.

A Jos, babban birnin Filato, an ga dogayen layuka a tsirarun gidajen man da ke sayar da man kuma bayanai na cewa suna sayarwa kan N800.

BBC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here