‘Muna shirin mayar da yan gudun hijira 6000 gida daga Chadi da Kamaru’ 

0
137

Gwamnatin Najeriya ta ce tana shirin mayar da ‘yan gudun hijirar ƙasar aƙalla 6000 daga ƙasashen Chadi da Kamaru.

Kwamishinan hukumar kula da ‘yan gudun hijira (NCFRMI), Tijjani Ahmed ne ya bayyana haka ranar Talata a Abuja a karshen wani da aka shirya don mayar da ‘yan gudun hijirar Najeriya gida. 

Ya ce kimanin ‘yan gudun hijira 21,000 ne ke a ƙasar Chadi yayin da Kamaru ke da wasu 14,000.

Ahmed ya ƙara da cewa za a mayar da mutane 6,000 daga Chadi zuwa gida yayin da za a tantance adadin waɗanda za a mayar da su daga Kamaru kafin a fara shirin wanda ake sa ran kammalawa nan da watanni biyu masu zuwa.

“Muna shirin mayar da waɗanda suke da sha’awar komawa gida, an kuma ƙulla yarjejeniya tsakanin hukumar UNHCR da gwamnatin Kamaru da kuma gwamnatin tarayya kan batun mayar da mutanenmu gida daga Kamaru,” in ji shi. 

Ya ce ana tattaunawa da gwamnatin jihar Borno kan wajen da za a ajiye ‘yan Najeriya da za a mayar da su gida, inda ya ce a yanzu haka ana gina gidaje a Banki da Baga domin ajiye su.

A cewarsa, galibin ‘yan gudun hijirar sun rasa matsugunansu ne sakamakon ambaliyar ruwa a 2022, rikicin Boko Haram, rikicin manoma da makiyaya da kuma kalubalen sauyin yanayi a yankin Arewa maso Gabas.

Mataimakiyar hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya, Bernadette Muteshi, ta yaba wa gwamnatin tarayya bisa jagorantar aikin mayar da ‘yan gudun hijirar.

BBC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here