Sojojin Rasha sun shiga sansanin dakarun Amurka a Nijar

0
218
Nijar Amurka

Sojojin Rasha sun shiga sansanin dakarun sama da Amurka ke amfani da shi a Jamhuriyar Nijar bayan matakin da mahukuntan Yamai suka ɗauka na yanke hulɗar soji da ita, kamar yadda wani babban jam’i a ma’aikatar tsaron Amurka ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Sojojin da ke mulkin Nijar sun umarci Amurka ta kwashe dakarunta kusan 1,000 daga ƙasar, wadda kafin juyin mulki ta kasance ƙawarta a yaƙi da masu tayar da ƙayar-baya na yankin Sahel waɗanda suka kashe dubban mutane tare da raba miliyoyi da muhallansu.

Wani babban jami’in tsaron Amurka, wanda ba ya so a ambaci sunansa, ya ce sojojin Rasha ba sa yin wata hulɗa da dakarun Amurka da ke sansanin. Hasalima suna amfani da wata ƙofa ta daban a sansanin mai suna Airbase 101, wanda ke kusa da filin jirgin saman ƙasa da ƙasa na Diori Hamani da ke Yamai.

Wannan mataki ya sa dakarun Rasha da na Amurka suna zaune a inuwa ɗaya, a yayin da ƙasashen biyu suke ci gaba da samun rashin jituwa sakamakon yaƙin Ukraine.

Kazalika lamarin ya sanya fargaba game da tsaron na’urorin Amurka a sansanin.

“Lamarin ba mai daɗi ba ne amma dai ba mai ɗorewa ba ne,” a cewar jami’in.

Ofisoshin jakadancin Nijar da Rasha da ke Washington ba su ce uffan game da batun ba lokacin da aka tuntuɓe su.

Mahukunta da dama a Afirka sun kori dakarun Amurka da na ƙawayenta daga ƙasashensu bayan juye-juyen mulkin da sojoji suka yi a ƙasashen waɗanda suke nesanta kawunansu da ƙasashen Yamma.

A yayin da dakarun Amurka ke shirin ficewa daga Nijar, tuni mahukunta a Chadi suka kore su daga ƙasar, yayin da kuma Nijar da Mali da Burkina Faso suka kori sojojin Faransa daga ƙasashensu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here