Rundunar Hisbah ta dauki hanyar kawo karshen Caca a Kano

0
70

Rundunar Hisbah ta Kano ta nemi al’ummar jihar su rika kawo mata bayanan guraren da ake aiwatar da haramtacciyar Sana’ar caca a fadin Kano.

Hisbah tace ta haka ne za’a samu damar tsaftace unguwanni daga matsalar rashin tarbiyya da kuma kaucewa afkuwa cikin fushin Ubangiji (SWA).

Mataimakin babban kwamandan rundunar Dr Mujahiddin Aminudden, ne ya sanar da hakan cikin wani jawabin daya gabatar bayan samun nasarar kama masu bude shagunan yin Caca a mayankar Abbatuwa dake kofar Mazugal, da kasuwar kofar wambai, sai wadanda aka kama a unguwar Sheka.

Karanta karin wasu labaran:Umar Bush da Alhaji Rufa’i sun ziyarci hukumar Hisbah ta Kano

Dr Mujahiddin Aminudden, yace an kama mutanen bayan samun umarnin yin kamen daga kotu.

Ya kuma tunatar da al’umma cewa yin Caca haramun ne a fadin Jihar Kano, Kuma tuni aka mika wadanda aka kama zuwa ga bangaren shari’a don yi musu hukuncin da addinin muslinci ya tanadar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here