Sayen ƙuri’u ya mamaye zaɓen gwamnoni da aka kammala – Rahoto

0
96

Cibiyar Dimokradiyya da ci gaba ta Najeriya CDD ta ce matsalolin sayen ƙuri’u da kuma tashin hankali sun mamaye zaɓen gwamnoni da na ƴan majalisar dokokin jihohi na ranar Asabar.

Cikin wata sanarwa da shugaban Cibiyar nazari kan zaɓe ta CDD, Farfesa Adele Jinadu da Daraktar cibiyar, Idayat Hassan suka fitar, cibiyar ta ce hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC ta fi yin ƙoƙari ta ɓangaren jigilar kayan aiki abin da ya sa aka samu isar kayayyakin zuwa rumfunan zaɓe a kan lokaci.

CDD ta kuma koka kan matsalolin sayen ƙuri’u da tashin hankali da yi wa masu zaɓe barazana da aka samu a yayin zaɓen a wasu jihohi kamar Kano da Jigawa da Legas da Enugu da Bayelsa da Rivers da kuma Yobe.

Masu sa idon da cibiyar ta aike zuwa jihohin bakwai sun bayar da rahoton samun wuraren da wakilan jam’iyyu suka sayi ƙuri’u.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here