Leicester da Everton na cikin hadarin rikitowa a gasar Firimiya

0
110

Dukkannin kungiyoyin sun shiga wasan ne a matsayi mara armashi a teburin gasar, amma maki daya da Leicester ta samu ya dan daga ta zuwa matsayi mai dan dama-dama, a yayin da Everton ke a matsayi na 19 har yanzu.

Dominic Calvert-Lewin na Everton ne ya fara cin kwallo, da bugun daga-kai-sai-mai-tsaron-raga, bayan da dan wasan bayan Liecester, Timothy Castagne ya girbe shi.

Sai dai bayan minti 7 kacal Caglar Soyuncu ya farke wa masu masaukin baki.

Bayan mintina 33 kuma Liecester ta  kara wata kwallo ta hannun Jamie Vardy, amma kafin a tashi wasa, dan wasan Najeriya, Alex Iwobi ya rama wa Everton.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here