Masu shirin ‘Mata A Yau’ sun ziyarci malam Daurawa

1
202

A makon da ya gabata ne dai kafafen sada zumunta a Arewacin Najeriya suka cika da zazzafar muhawara kan wani shiri mai take ‘Mata A Yau’ da ake gabatarwa a gidan talabijin na Arewa24. 

Hakan ya samo asali ne daga bayanin da ɗaya daga cikin masu gabatar da shirin, Aisha Umar Jajere ta yi dangane da batun gaisuwa tsakanin mata da miji.

Abinda aka fadi a shirin Mata A Yau A cikin wani ɗan gajeren bidiyo da aka wallafa a shafin ‘Mata A Yau’ na Facebook, an ga ɗaya daga cikin matan na cewa, idan mata ba ta gaishe da mijinta ba shi sai ya gaisheta, wanda hakan ne ya janyo zazzafar muhawara.

Malamai da dama a ciki da wajen birnin Kano, sun yi martani mai zafi dangane da wannan kalami da ma sauran abubuwan da aka gabatar a shirin. 

Haka nan ma ma su amfani da kafafen sada zumunta musamman ma Facebook a Arewacin Najeriya, sun caccaki masu gabatar da shirin inda mafi yawa ke ganin hakan na iya janyo rigingimu a tsakanin ma’aurata.

Biyo bayan suka da masu gabatar da shirin suka sha daga ɓangarori daban-daban, sun kai ziyara wajen kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa.

Sun bayyana cewa kuskure aka samu, amma ba abinda suke son isarwa ba kenan, inda suka bayyana cewa hankalinsu ya tashi sosai kan yadda jama’a suka taso mu su. 

Fitaccen malamin nan na addinin Musulunci, Sheikh Adam Abdallah Adam ne ya bayyana hakan a cikin wani ɗan gajeren bidiyo da wani mai amfani da kafar X, @A_Y_Rafindadi ya wallafa.

Ya ce sun nemi al’ummar Musulmin da kalaman da suka yi a cikin shirin suka ɓatawa rai da su yi haƙuri.

1 COMMENT

  1. Muna Malan yayi musu Tarbiyya irin ta Addinin Musulunci kafin su bar office kan cewa Namiji shine Jagora a Gidan Aure ba Mace ba

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here