Hukumar da ke kula da kwararrun malaman makarantu a Najeriya ta sanar da cewar hare haren ‘yan ta‘addan boko haram ya yi sanadiyyar mutuwar malaman makarantu dubu 2 da 295 tsakanin shekarar 2009 zuwa 2022.
Babban jami’in Hukumar Farfesa Josiah Olusegun Ajiboye ya gabatar da wadannan alkaluma masu tayar da hankali lokacin da ya ke jawabi wajen taron kungiyar malaman makarantu na kasa a Najeriyar.
Ajiboye ya ce ayyukan ta’addanci sun tilasta rufe makarantu sama da 1,500 abinda ya haramtawa dalibai sama da dubu 600 zuwa karatu domin samun ilimi.
Jami’in ya roki gwamnatin Najeriya da ta sake fasalin tsaron kasar domin samar da tsaron da ake bukata wajen kare malamai da dalibansu a sassan kasar da ake fama da tashe tashen hankula.
Ajiboye yace a matakin farko, ya dace gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi da kuma tarayya da su gaggauta aiwattar da shirin kasa na samar da tsaro a makarantu ta hanyar ware wani kashe na kudin kasasfin su da zai kula da wannan bangare.
RFI