Kamfanin Mai na NNPCL ya kulla yarjejeniyar gyaran Matatar Mai ta Kaduna da kamfanin Daewoo Group na kasar Koriya ta Kudu.
Shugaba Muhammadu Buhari, ya bayyana wa taron sanya hannun burinsa na ganin an, “Kammala ayyukan matatun man Warri da Kaduna da kuma jiragen dakon iskar gas.
“Tabbas hakan zai bayar da karin dama ga Daewoo da sauran kamfanonin kasar Koriya ta Kudu a Najeriya.”
Fadar Shugaban Kasa ta Ruwaito shi yana cewa, “Na san Daewoo Group babban kamfani ne da ke gudanar da harkokinsa a bangaren motoci da sufurin jiragen ruwa da sauran bangarori.
Buhari, ta bakin kakakinsa, Femi Adesina, ya ce, “Ina kuma godiya bisa kwarin gwiwa da kuke da shi a kan Najeriya,” in ji Shugaba Buhari ga kamfanin.
Shugaban kasar da jami’an gwamnatin Najeriya sun je Koriya ta Kudu ne domin halartar taron farko kan sarrafa tsirrai na duniya da aka gudanar a kasar.