Yayin da ya rage kwanaki biyu kacal a fara gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya na shekarar 2022 a Qatar, rahotanni sun ce kasar mai masaukin baki ta matsa wa FIFA lamba kan ta haramta sayar da barasa a filayen wasanninta takwas.
Jaridar Times ta ruwaito cewa jamiāan Qatar sun bude tattaunawa da FIFA da kuma mai samar da kayayyaki Budweiser kan dakatar da sayar da giyar gaba daya a kusa da filayen wasa.
Ana sa ran yanke shawara ta karshe daga baya a ranar Jumaāa, kodayake rahotanni sun nuna cewa haramcin zai iya ci gaba.
Ganin cewa Budweiser ya kasance daya daga cikin manyan abokan huldar FIFA, irin wannan haramcin kan kayayyakin nasu zai kawo cikas kan hakan.