Majalisar dattawan Kenya ta umarci sanatoci mata guda biyu da su fice daga zauren majalisar, saboda tufafin da suka sanya a lokacin da suka halarci zaman majalisar.
ÆŠaya daga cikinsu ta saka riga marar hannu, É—ayar kuma saboda ganin É—igon jini a wandonta kasancewar tana al’ada.
Sanata Gloria Orwoba ta shaida wa shugaban majalisar cewa lamarin jinin al’ada abu ne da ke aukuwa ga mata ba tare da sun shirya masa ba.
To amma an umarce ta da ficewa daga majalisar kasancewar ba a amince da ganin É—ingon jini a tufafi ba, dan haka dole ta sauya tufafi.
An kuma umarci takwararta Sanata Karen Nyamu da ta fice daga zauren majalisar sakamakon sanya riga marar hannu.
Sanatocin ɓangaren adawa sun yi ƙorafin cewa Ms Nyamu ta sanya tufafin da zai kawo rashin kunya a majalisar.
Shugaban Majalisar ya ce hakan saɓa wa dokar sanya tufafi ce ta majalisar, wadda ta tanadi cewa dole mata su sanya tufafin da za su kare mutuncinsu.