Hukumar lafiya ta duniya Who dakuma Asusun tallafawa kananan yara na majalisar dinkin duniya sunyi na’am kan yanda ake gudanar da ayyukan rigakafin cutar Corona a jihar Kano.
Shugaban wata tawagar kungiyoyi masu zaman kansu karkashin hukumomin 2 Tedd Chambe ya bayyana hakan a wata ziyara da suka kaiwa gwamnan jihar Kano dakta Abdullahi Umar Ganduje a gidan gwamnati.
- Rikici a Ukraine ya wargaza makomar yara – UNICEF
- Makarantar Kimiya da Fasaha ta jihar Kano na cikin mummunan yanayi – ASUP
“Mun Kawo ziyara Kano ne domin duba yadda ake gudanar da allurar rigakafin Corona tare da duba yadda zamu iya taimakon jihar Ta fannin rigakafin” a cewar Tedd Chambe.
Da yake jawabi gwamna Abdullahi Umar Ganduje yace babu shakka cutar corona ta taba rayuwar al’umma da dama ta fuskar lafiya da tattalin arziki adon hakane jihar Kano zata cigaba da daukar matakan dakile ta.
Anasa jawabin kwamishinan lafiya Na jihar Kano Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa yace gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci kungiyoyin da su hada karfi da karfe da gwamnatin wajen samar da cibiyar kawo allurar rigakafin corona a jihar domin magance karancin allurar rigakafin a jihar.