HomeLabaraiAmbaliya ta yi awon-gaba da gawawwaki 500 a jihar Neja

Ambaliya ta yi awon-gaba da gawawwaki 500 a jihar Neja

Date:

Related stories

Manyan kabilar Fulani suna so su ga bayana – Gwamna Ortom

Gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom ya koka da cewa...

Kotu ta raba auren ‘yar Ganduje da shafe shekaru 16

Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Kano...

Kotu ta aike da Murja Kunya zuwa gidan yari

Wata kotu a Kano ta aika da Murja Ibrahim...

Al’ummar garin Mariga da ke karamar hukumar Bariga a jihar Neja da ke Najeriya na kan neman gawawwaki sama da 500, da ake fargabar ambaliya ta yi awon gaba da su daga wata makabarta da ke garin.

Babban limamin Mariga Alhaji Alhassan Na’ibi ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga BBC Hausa a yau Laraba.

”Ambaliyar ruwa ta lalata kaburbura fiye da 1500, amma an sake binne gawawwaki kimanin dubu daya”, in ji limamin.

Ya kara da cewa yanzu haka ana neman sama da gawa 500 da suke tunanin ambaliya ta yi gaba da su a makabartar Mariga.

To amma limamin ya ta’allaka matsalar da aikace-aikacen masu hakar ma’adanai a kusa da makabartar, don a cewarsa ba su taba fuskantar yanayi irin wannan ba a sama da shekaru 60.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories