Zamu tabbatar da anyi sahihin zabe a 2023 – Buhari

0
72

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake jaddada aniyar gwamnatin sa na gudanar da karbabben zabe a shekara mai zuwa domin zabo wanda zai maye gurbin sa a matsayin shugaban kasa.

Buhari ya bayyyana haka ne ga taron majalisar Dinkin Duniya dake gudana a New York, bayan ya koka akan yadda shugabannin wasu kasashe ke sauya kundin tsarin mulki domin ci gaba da zama a karaga.

Shugaban Najeriyan wanda ya jinjinawa kawayen kasar akan irin gudumawar da suke bata wajen ganin dimokiradiya ta zauna da gindinta, yace daya daga cikin abin tarihin da zai baiwa jama’ar kasar, shine gudanar da karbabben zabe a watan Fabarariru mai zuwa.

Buhari ya shaidawa taron Majalisar cewar, a irin wannan lokaci a shekara mai zuwa, wani sabon shugaban kasa ne zai tsaya a gaban su domin gabatar da jawabi a madadin Najeriya.