Buhari ne ya hana saka sunan Osinbajo a kwamitin yakin neman zaben Tinubu – APC

0
100

Jam’iyar APC da ke mulki a Najeriya ta bayyana dalilan da suka sanya ba a sanya sunan mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na Asiwaju Bola Tinubu ba.

A cikin wata sanarwa da kakakin tawagar yakin neman zaben Tinubu Festus Keyamo ya fitar a ranar Asabar din nan, ta ce shugaban kasar Muhammadu Buhari da kansa ne ya hana sanya sunan Osinbajo da sakataren gwamnatin kasar Boss Mustapha don su mayar da hankali a sha’anin tafiyar da gwamnati.

Rashin ganin sunan mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo a jerin sunayen mutane 422 da ke cikin kwamitin yakin neman zaben na Tinubi ya haifar da cecekuce a sassan Najeriya, ganin yadda Osinbajo ke cikin wadanda suka kalubalanci Tinubu wajen neman tikitin tsayawa jam’iyar takarar shugaban kasa.

Sai dai anga sunan tsohon ministan sifuri na kasar Rotimi Amaechi a cikin jerin sunayen, duk da cewa shi ne ya zo na biyu a zaben fidda gwanin na jam’iyyar ta APC mai mulki.

 

RFI.